22 Disamba 2021 - 13:23
​Yemen: An Rufe Filin Jirgin Sama Na San’a Bayan Da Saudiyya Ta Kai Da Jiragen Yaki A Kansa

Wani jami'in gwamnatin Sana'a a kasar Yemen ya sanar da cewa, an dakatar da gudanar da aikin filin jirgin Sana'a sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya suka kaddmar a kan filin jirgin saman na Sanaa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - bayar da rahoton cewa, Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sanar da cewa, bayan harin da jiragen yakin kawancen Saudiyya suka kai a filin jirgin saman birnin Sanaa a daren jiya, an rufe filin sauka da tashin jiragen saman gaba daya, sannan kuma an dakatar da dukkan jiragen agaji na MDD da sauran jiragen jin kai sauka da tashi a wurin.

Raed Jabal mataimakin babban daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na gwamnatin ceto kasar Yemen ya bayyana cewa: jiragen yakin Saudiyya sun yi ruwan bama-bamai kai tsaye a filin jiragen sama na Sana'a da daddare, sakamakon haka aikin filin jirgin ya tsaya gaba daya.

Ya kuma jaddada cewa, manufar Saudiyya a wannan harin ita ce hana kai kayan agaji ga al'ummar Yemen da kuma hana jiragen Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa da ke aiki a kasar ta Yemen.

Ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin gaggawa don dakile hare-haren da kawancen Saudiyya ke kai wa a filin jirgin saman Sanaa, wanda ya kawo cikas ga ayyukansa.

Rundunar kawancen Saudiyya ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya cewa ta kai harin bam a wurare shida a filin jirgin saman Sanaa.

342/